Majalisar wakilai ta bukaci ministan sadarwa ya bayyana a gabanta domin yin bayani akan tarar da hukumar ta ci MTN

Majalisar wakilan Najeriya ta bukaci Ministan sadarwa Mr. Adebayo Shittu da shugaban hukumar sadarwa ta kasa NCC, farfessa Garba Danbatta, su bayyana a gaban majalisar domin yin bayani akan tarar Naira Tiriliyan 1.04 da hukumar NCC ta ci kamfanin sadarwa na MTN.

An dai dauki wannan matakin ne a ranar litinin a wani taron masu ruwa da tsaki wanda kwamitin majalisar mai kula da fasahar sadarwa ya shirya.

Yayin da shugaban Kwamitin Saíd Fijabi yake sanar da shawarar da kwamitin ya yanke yace bai kamata ma’aikatar da hukumar su yadda da ragi akan tarar da a ci kamfanin na MTN ba.

Mista. Fajabi ya bayyana cewar ”mun yi mamaki da muka ji cewa  Kamfanin MTN zai biya tarar Naira biliyan 330. Ta yaya zai biya wadannan kudade bayan ministan ya fada mana cewa an dakatar da komai sai mun kammala bicikenmu? A matasayinmu na majalisar wakilai, ba mu yadda da wannan ragin tara da aka yi wa kamfanin MTN ba, saboda dokar hukumar NCC ba inda tace a rage tara.

Hukuamar kula da harkokin sadarwa ta kasa a Najeriya ta ci kamfanin MTN tarar Naira Triliyon 1.04 ne sakamakon kin rufe layukan wayar wadanda basu yi rijista ba.

Amma hukumar da kamfanin MTN suka sasanta a tsakaninisu a ka rage tarar ta koma Naira Biliyan 330.

Kwamitin dai ya bukaci Ministan sadarwa da takwararsa da maáikatar sharia, da kuma Shugaban hukumar Sadarwa dama duk masu ruwa da tsaki akan yarjejeniyar rage tarar da su bayyana a gaban majalisar, a ranar litinin ga watan Yunin da muke ciki.

 

Abdulkarim Rabiu.