Majalisar Zartarwar Najeriya ta na ganawa akan kasafin kudi na 2016

Yan zu haka dai majalisar zartarwa tarayyar Njeriyar na ganawa a fadar shugaban kasa dake Abuja babban birnin kasar. Ministan yada labarai da al’adu Lai Mohammed ya ce “ taron ya mai da hankali ne kacokan akan kasafin kudin Najeriya na 2016’’
Ya kara da cewar majalisar zata yi la’akari da kasafin kidin ne ta yadda zai amfani ko wace ma’aikata.
A ranar Alhamis ne dai Majalisar dokoki ta aika wa shugaban kasar cikakken bayanin kasafin kudin a karo na biyu.
Tun da fari majalisar ta aike wa da shugaba Buhari takaitaccen bayanin kasafin kudin amma ya dawo wa da mahukuntan.
Ya zuwa lokacin da aka hada wannan rahoto, ministocin sun tafi gajeren hutu domin Musulmai su sami damar zuwa sallar Juma’a.
Ministan yada labarai da al’adu Lai Muhammed ya fadawa manema labarai cewar zai fadi Karin bayani bayan an kammala taron.
Taron wanda mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ya jagoranta, ya sami halartar Ministoci da shugabannin sashe-share da hulumomi na tarayya da ma wasu daga cikin masu bai wa shugaban kasa shawara ta musamman.

 

ABDULKARIM