Ministan Abuja ya sha alwashin samar da gidaje 400 ga ma’aikatan gwamnati duk shekara.

Gwamnatin babban birnin tarayya ta bayar da tabbacin samar da gidaje 400 duk shekara ga ma’aikatan gwamnatin dake yankin babban birnin.

 

Ministan Abuja Malam Muhammad Musa Bello wanda ya bayyan hakan yayin da yake karbar bakuncin shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya Ms. Winfred Ekanem Oyo-Ita, a garin Abuja babban birnin Najeriya, yace an riga an ware kudaden da za a gina gidajen a cikin kasasfin kudin babban birnin tarayya na wannan shekarar domin fara aikin ba tare da bata lokaci ba da kuma inganta jin dadin rayuwar maáikatn gwamnati.

 

Hari la-yau Malam Bello ya bayyana cewar a tun da aka nada shi ministan babban birnin tarayya, ya lura cewa kananan ma’aikatan da basu da gidade mallakar kansu suna dunbun yawa a cikin garin Abuja.

 

Ya ce wasu daga cikin ma’aikatn ma sun shafe shekaru suna neman filaye abin yaci tura, dalidin da ya sa kenan suke zama a gidajen haya.

 

“Kafin a dana ni minista na dauka cewa duk mazaunin birnin tarayya ya mallaki gidan kansa. Amma a bin mamaki, na fahimci cewa ma’aikata da yawa musamman ma kanana da matsakaita basu mallaki guidajen kansu ba’’, in ji minister.

 

Da yake maida martini ga bukatar da shugabar ma’aikatan gwamnati tarayya ta nema na samar da filin da za a gina gidajen maaikata da yawa karkashin shirin samar da gidaje ga ma’aikatan babban birnin tarayya, minisrtan ya bayar da tabbacin cewa gwamnati a shrye take ta hada gwiwa da ofishin shugaban ma’aikatan gwamntin tarayyar domin cimma burinta.

ya kara da cewa gwamnatin babbana birnin tarayya ta kammala shirye-shiryenta na farfado da shirin samar da gidaje masu yawa domin amfanar ‘yan Najeriya musamman ma’aikatan gwamnati.

Malam Bello ya ce sabon tsarin shirin samar da gidajen an tsara shi ne ta yadda zai samar dukkan ababen more rayuwa da ake bukata a gidajen.

 

 

Abdulkarim Rabiu.