Morocco za ta koma Tarayyar Afurka

A hukumance kasar Morocco ta sanar da aniyarta na sake shiga kungiyar tarayyar Afurka.
A wani sako da kasar ta aike wa kungiyar da ke taro a kasar birnin Kigali na kasar Rwanda, Sarki Mohammad na shida yace lokaci ya yi da Morocco za ta sake komawa cikin iyalanta.

A shekarar 1985 ne Morocco ta fice daga kungiyar trayyar Afurka, a lokacin da aka kungiyar tai na’am da fafutukar da yankin yammacin Sahara ke yi.

Ya yin da ita kuma Morocco ta ce yankin yammacin Saharar ya fada ne cikin iyakarta.
Sai dai a ranar juma’a da ta wuce ne kungiyar tarayyar Afurka ta ce za ta ci gaba da fafutukar karbarwa mutanen yankin yammacin Saharar ‘yanci.

 

 

BBC/ Abdulkarim Rabiu