Mutane 28 sun mutu a harin Aleppo

Kungiyar sa ido kan kare hakkin bil’adama ta Syria ta ce wasu hare-haren sama da aka kai sun yi sanadin mutuwar a kalla mutane 28 a birnin Aleppo.

 

Rahotanni sun ce jiragen yakin Rasha ne suka kai hare-haren da nufin samun yankunan da ke karkashin ikon ‘yan tawaye a gabashin birnin.

 

Kamfanin dillanci labari na Faransa AFP, ya ce an yi ta jefa bama-bamai a yankuna da dama.

 

Cikin yankunan da bama-baman suka fada har da wani asibiti, inda marasa lafiya da ma’aikatan wajen da dama suka ji rauni.

 

Gwamnatin Syria ta ce ‘yan tawaye sun kai hare-hare a Yammacin birnin Aleppo da ke karkashin ikonta, inda mutum daya ya mutu.

 

Aleppo ya kasance cibiyar kasuwanci da masana’antu na Syria, amma tun shekarar 2012 ake gwabza fada a birnin.

 

BBC/Abdulkarim Rabiu.