Najeriya da Amurka za su bunkasa dagantar kasuwanci

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana cewar zata hada gwiwa da Amurka ta bangagen ayyukan kwadago da nufin bunkasa dangantar kasuwanci ta kasa da kasa a tsakanin kasashen biyu.

Ministan kwadago da ayyukan yi, sanata Chris Ngige ne ya bayyana hakan a yayin da yake karbar bakuncin jami’in kula da harkokin siyasa na ofishin jakadancin Amurka, Mr Marlin Hardinger, a Abuja babban birnin kasar.

Bayanin hakan na kunshe ne a wata sanarwa da maitamakin darakta yada labarai na ma’aikatar Kwadago da ayyukan yi, Mr Samuel Olowoookere ya fitar a garin Abuja.

Sanata Ngige yace shawarar da Amurka ta yanke na kara yaukaka dangantakar cinikayya da Najeriya ta fannin ayyukan kwadago zata tamaka mutuka wajen bunkasa fannin kasuwancin kasa da kasa a Najeriya.
’’muna mika godiyarmu ga Amurka dangane da daukar wannan mataki, abin alfahari ne mu ga yadda kuke hada kai da kungiyar kwadago ta kasa da kasa don samun nasarar wannan alaka ta kasuwanci.

’’Hakika hakan zai taimaka wajen bunkasa harkokin kasuwan ba a Najeriya kadai ba har ma nahiyar Afrika baki daya.’’ In Ji sanata Ngige.

Abdulkarim Rabiu