Najeriya da China sun kulla yarjeniyar fahittar juna ta fiya da dala biliyan 80

Ministan kasa kana babban daraktan kamafanin man fetur na kasa a Najeriya, NNPC, Dakta Ibe kachikwu wanda yanzu haka yake ziyara a matsayin wakilin shugaban Najeriya na musamman a kasar Sin wato China, shi ne ya bayyana hakan a wani taron masu zuba jari a kamfanin NNPC a kasar.

 

A cewarsa za a yi amfani da kudin ne wajen zuba jari a fannonin mai da iskar gas, da gina bututan mai, da matatu, da wutar lantarki, da kuma gyaran rijiyoyin mai.

 

Dakta Kachikwu, yayin da yake gabatar da jawabi a wajen taron na masu zuba jari fiye da 200 kan harkokin mai da iskar gas, ya jaddada cewa an shirya taron baje kolin ne a matsayin kare yaukaka yarjejeniyar da kasashen biyu suka kulla a lokacin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kai ziyarar aiki China cikin watan Afrilun, 2016.

 

Har-ila-yau ya yaba da kokarin da kokarin shugaba Muhammadu Buhari na ganin an sami sauyi a fannin mai da iskar gas.

 

Kazalika ya bayyana godiyarsa ga gwamnatin China da Masu zuba dangane da goyan bayan da suka bai wa Najeriya, wanda hakan yake kara bai wa fannin mai da iskar gas na kasar tabbaci a kasuwannin duniya.

 

 

Abdulkarim Rabiu.