Najeriya da China sun yi hada-hadar kasuwancin dala biliyan 14.9

A cikin shekara ta 2015 Najeriya da China sun yi hada-hadar kasuwanci na Dala Miliyan dubu 14.9.

Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed ya bayyana cewa kasashen biyu sun amnince su ci gaba hurdar cinikayya batare da ganin kyashi ba.

Mohammed ya bayyana hakan ne yayin da wakilan kamfanin watsa shirye-shiyen talabijin ta tauraron dan Adam Startimes na kasar China ya kai masa ziyarar ban girma ranar litinin a ofishinsa dake Abuja babban birnin Najeriya.

“Najeriya tana iyakar kokarinta don ganin ta kara janyo hankalin masu zuba jari daga Kasar China musamman wadan da zasu kafa masana’antun da zasu samar da ayyukan yi a kasar” in ji Minista

“A wani taro da muka gudanar kwanan nan a matsayinmu na kasa, mun rattaba hannu a kan wata jarjeniya a tsakanin kasasken biyu. A jarjejeniyar, China ta amince ta fara irin wadannan ziyarce-ziyarce da kuma hadin gwiwa da kasashen Afrika.

‘’ Mun yi jarjejeniya akan bunkasa ababen more rayuwa, alal misali samar da fitulun kan hanya da danjojin bada hannu masu amfani da hasken rana a Abuja, babban birnin Najeriya, da gina babbar hanyar mota daga Calaba zuwa Lagos, da layin dogo na Kano zuwa Lagos, da kuma gagugauta aikin layin dogo mai amfani da wutar lantarkin a cikin garin Abuja”. A cewar Mohammed.
A kokarin da ma’aikatar yada labaran ke yi na ganin ta sauya fasalin tsarin kafafan yada labarai izuwa na zamani, kasar China ta yarda ta yi aiki da Najeriya domin samun nasarar wannan aiki.

Har-ila-yau, ministan ya jaddada matsayinsa akan aikin sauya fasalin tsarin yada labarai izuwa na zamani inda yace yana nan daran kuma babu gudu babu ja da baya.

Shima da yake nasa jawabin mataimakin shugaban kamfanin Startimes, Zhao Yuegin ya ce kamfanin a shirye yake ya yi aiki da Najeriya domin cin nasarar wannan aiki.

Abdulkarim Rabiu.