Najeriya ta nemi goyon bayan kungiyar kwadago ta kasa da kasa.

Gwamnatin Najeriya ta bukaci goyan bayan kungiyar kwadago ta kasa da kasa (ILO), wajen bunkasa ma’aikatu da sanin makamar aiki, domin tabbatar da samun kyakyawan yanayin aiki da kuma ci gaban kasa mai dorewa.

Ministan Kwadago da ayyukan yi, Dakta Cris Nigige ne ya bukaci hakan yayin da ya kai ziyarar aiki a ofishin Babban Daraktan kungiyar ILO, Guy Ryder dake Geneva babban birnin Gwitzerland.

Ziyarar dai na daya daga cikin wani banagare na babban taron kungiyar karo na 105 da yake gudana a birnin na Geneva.

“muna neman taimakonku ta bangaren bayar da hadin kai, Muna so mu nemi goyon bayan ILO ta bangaren wajen bunkasa ma’aikatu da sanin makamar aiki.

“Sauran bukatun mu sun hada da goyon bayan majalisar sasansata riciki, da bangaren gwamnati da kanfanoni masu zaman kansu, da kotun kasa mai kula da sasanta rikicin masana’antu da ma’aikata da kuma batutuwa makamantan wannan.

Har-ila-yau muna so mu ga an tabbatar da shirin bunkasa tattalin arziki, don samar da ayyukan yi a yankunanmu na karkara,” In Ji Dakta Ngige.

Ministan ya bayyana cewar a lokuta da dama gwamnati ta gana da Mataimakin Babban Daraktan sashen ayyuka na Kungiyar kwadago ta kasa da kasa(ILO) da kuma Mataimakin Babban Daraktan sashen gudanarwa agame da hanyoyin da za a ciyar da alámuran da suka shafi kwadago gaba.

‘Mafi yawancin batutuwan da muka tattauna mun yi su ne da nufin neman taimakon shirye-shiryen da za su ciyar da kasarmu gaba,” In ji Ministan.

 

 

Abdulkarim Rabiu.