Najeriya za ta karfafa alakar kasuwanci da Italiya

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana dangantakar dake tsakanin Najeriya da Italiya a matsayin mai karfi, yayin da ya bukaci yaukaka alakar kasuwanci da tattalin arziki a tsakanin kasashen biyu.

Shugaban ya yi wannan kiran ne a fadarsa dake Abuja babban birnin kasar, yayin da Ministan harkokin wajen Italiya Mista Poalo Gentiloni ya kai masa ziyarar ban girmi.

Har-wa-yau shugaba Buhari ya bayar da shawar cewa kamata ya yi a maida hankali wajen yaukaka dangantakar dake tsakanin Najeriya ta Italiya.

Shugaban na Najeriya ya kuma yaba da irin harkokin da Italiya take yi a Najeriya na gaggauka zuba jari a harkokin kasuwanci, sannan ya bayyana jin dadinsa dangane da kokarin da kasar ke yina na bullo da wasu sabbin hanyoyin kasuwanci a kasar.

Kazalika ya yaba da irin goyon bayan da Italiya ke bai wa gwamnatin Najeriya wajen tunkarar ayyukan jin kai a yankin arewa masu gabas da kuma horon da Itliyawa ke bai ‘yansandan Najeriya.

Shi ma da yake nasa jawabin, Mista Gentiloni, wanda ministan harkokin cikin gidan Italiya Mista Domenico Manzione ya rufa wa baya, ya bayyana tallafin jin kai na dala miliyan 10 da gwamnatinsa ta bai wa kasashen dake yankin Tafkin Chadi ba ya ga wanda ta ke bayar wa a cikin tsarin tallafin da kungiyar tarayyar Turai EU ke bayar wa.

 

Abdulkarim Rabiu