Najeriya zata gaggauta aiwatar da kasafin kudin 2016

Mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ya bayyana cewa gwamnati na iyakar kokarin samar da kudade domin gaggauta aiwatar da kasafin kudi na 2016.

 

Farfessa Osinbajo ya bayyana hakan ne a fadar shugaban kasa dake Abuja babban birnin kasar, yayin da yake ganawa da wata tawagar kwamitin sayar da hannun jari a kamfanonin gwamnati ga yan kasuwa karkashin jagorancin shugaban kwamitin Malam Ahmed Yarima.

 

Mataimakin shugaban kasar ya bai wa manbobin kwamitin tabbacin  cewa Gwamnatin Shugaban Muhammadu Buhari zata tabbatar da cewar an gudanar da shirin sayar wa da yankasuwa kamfanonin gwamnati cikin gaskiya da adalci.

 

‘’gaggautawar ma tana da mahimmaci a wureren da suka wajaba, har ma da hanyoyin samun kudaden aiwatar da kasafin kudin na 2016, saboda hanyoyin da muke da su ahalin yanzu suna daukar lokaci mai tsawo’’ in ji Mataimakin shugaban kasar.

 

Har ila yau farfessa Osinbajo ya bayyana cewar fadar shugaban kasa za ta yi aiki tare da majalisar dokoki domin gaggauta amince wa da kudirin dokokin da suke da nasaba da sayar da kamfanonin gwamnati ga ‘yan kasuwa ciki kuwa har da kudirin dokar da ta bai wa masu zuba jari damar bayyana ra’ayoyinsu na yin kasuwanci.

 

Da yake zantawa da Muryar Najeriya bayan kammala taron Shugaban kwamitin Malam Ahmed Yerima ya ce wajibi ne kamfononi masu zaman kansu su yi aiki tare da gwamnati domin bunkasa harkokin kasuwanci a Najeriya.

 

Malam Yarima wanda shi ne ke wakiltar mazabar Missau da Dambam a majalisar wakilai ta tarayyar Najeriya ya ce taron ya amince a bar kamfanonin da ba na gwamnatin ba su gudanar da harkokin kasuwancinsu yayin da gwamnati za ta rika lura da su.

 

Ya ce an fada musu cewa nan ba da jima wa ba za a kaddamar da majalisar kula da sayar da hannun jari ga kamfanonin gwamnati ta kasa.

 

 

Abdulkarim Rabiu.