ZA A KADDAMAR DA KWAMITOCI AKAN AYYUKAN CI GABA NA HADIN GWIWA TSAKANIN NAJERIYA DA CHINA.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin gaggauta kaddamar da kwamitocin domin su kammala tattaunawa akan sabbin ayyukan ci gaba na hadin gwiwa tsakanin Najeriya da China, da suka hada da wutar lantarki, da ayyukan gona, da masana’antu, da kuma albarkantun kasa.

Shugaban ya bayar da umarnin hakan ne a garin Beijing na kasar Sin Wato China bayan kammala tatunawa tsakanin wakilansa da manyan Jami’an gwamnatin China, karkashin Jagorancin Shugaba Xi Jinping.

Nan da zuwa karshen wannan watan ne dai ake sa ran kwamitocin zasu kammala aikinsu.

Tun da fari, yayin da yake gabatar da jawabinsa shugaba Buhari ya yi maraba da kudirin Chaina na tallafawa Najeriya a kokarin da ta ke yin na bunkasa tattalin arziki ta yadda zata iya gogayya da sauran kasashen duniya da suka ci gaba.

Shi ma da yake nasa jawabin shugaba Jinping, ya bayyana cewar ya yi na’am da shawarar da Najeriya ta yanke na kara fadada tallalin arzikinta a maimakon dogaro da man fetur.

Bunkasa ababan more rayuwa

Domin taimakawa Najeriya cimma wannan buri, China ta sha alwashin bai wa kasar cikakken goyan baya ta fannin samar da ababan more rayuwa da ayyukan ci gaban rayuwar al’umma.

Kazalika kasar China ta bayyana kudirinta na gudanar da ayyukan ci gaba da yawa a Najeriya, kamar gina matatun mai, da tashoshin wutar lantarki, da kanfanonin sarrafa ma’adanai, da masaku da kuma masana’antun sarrafa abinci.

Da yake maida martini ga kudirin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari na mai da Najeriya kasar da zata rika dogaro da abincin da take samar wa da kanta, shugaba Jinping ya bayar da tallafin Dala miliyan goma sha biyar ga Najeriya, domin fara kaddamar da ayyuka a gonaki 50 na gwaji dake duka fadin kasar.

Har-wa-yau Najeriya da China sun amince su karfafa musayar sojoji da ma’aikantan gwamnati a adaya daga cikin wani babban shirin na bunkasa ma’aikata don sanin makamar aiki.

Tallafin karatu

Ta wannan fanni, China ta yi alkawarin kara yawan tallafin da take bai wa dalibai yan Najeriya duk shekara daga 100 zuwa 700. Bugu da kari zata rika bai wa yan Najeriya 1000 gurbin samin horo a kasar China a duk shekara.

Shugaba Jinping ya kuma yaba da yaki da cin hanci da shugaba Buhari yake yi.

kasalika shugaban Chinan ya kuma tabbatar wa da shugaba Buhari cewar a koda yaushe Najeriya zata rika samun kulawa ta musamman akan harkokin da suka shafi gwamnatin kasar China.

 

ABDULKARIM RABIU