Najeriya zata kammala ayyukan ci gaba da aka fara cikin shekaru uku.

Ministan wutar lantarki da ayyuka da gidaje Babatunde Raji Fashola, ya bayyana cewar gwamnatin tarayya ta dukufa wajen ganin ta kammala duka manyan ayyukan ci gaba da yanzu haka suke gudana cikin shekaru uku.

Fashola ya bayar da tabbacin hakan ne yayin da ya kai ziyarar gani da ido a aikin ginin gadar da ta hada garuruwan Loko da Oweto dake jihohin Nasarawa da Beniwai.

Ya ce gwamnatin tarayya zata samar da kudaden biyan masu kwantiragin da zarar sun kammala ayyukansu.

“Gwamnatin tarayya da Shugaba Muhammadu Buhari sun bayyana kudirinsu na kammala dukkan ayyukan ci gaba da yanzu haka suke gudana da kuma wadanda tuni aka manta da su.

“zamu maida hankali wajen kammala ayyukan da yanzu haka suke gudana, wannan na daya daga cikin ayyuka da dama da suke gudana.

“tagwayen titin Lagos zuwa Ibadan na daya daga cikinsu; sai na Kano zuwa Maiduguri; da na Iloron zuwa Jebba, da kuma gadar Niger ta biyu na daya daga cikin ayyukan.

’’Dukkan wadannan ayyukan yanzu haka ‘yan kwangila sun koma bakin aiki, kuma zasu fara aiki. Sannu-sannu nan da shekaru uku zamu kammala su da yardar ubangiji”. In ji Minista.

Har-wa-yau Fashola ya bayyana kwarin gwiwarsa kan cewa wadannan ayyukan zasu bunkasa ababen more rayuwa da kuma samar da ayyukan yi, da damarmakin kasuwanci ga Jama’a.

 

 

Abdulkarim Rabiu