Najeriya zata zama cibiyar fasahar yada labarai ta zamani a Afrika

Hukumar dake kula da ci gaban fasarar yada labarai ta zamani a Najeriya NITDA, ta bai wa al’ummar kasar tabbacin cewa nan da shekaru 5, kasar zata zama cibiyar fasahar yada labarai ta zamani a nahitar Afrika.

Mai rikon mikamin babban daraktan hukumar Dakta Vincent Olatunji ne ya bayyana hakan yayin zantawarsa da Muryar Najeriya,  cewa Najeriya a  shirye take da ta yi amfani da fasahar kirkire-kirkire don ciyar da kasar gaba.

Mai rikon mikamin babban daraktan hukumar ta NITDA ya babbayana hakan ne don karfafa  gwiwar matasa wadanda suke da zimmar yin amfani da fasahar da Allah ya huwace masu kuma suke da kishin ci gaban kasa , in da ya ce abu ne mai yiyuwa Najeriya ta zama cibiyar fasahar yada labarai da sadarwa a Nahiyar Afrika.

Matasan Najeriya suna da kishin kasa da kuma kwazo, zasu iya sadaukar da kansu, wannan shi ne abin da fasahar kimiyya ke bukata, dole ka nuna shaáwarka. Ina hasashen cewa nan da shekaru 5 Najeriya zata zama cibiyar fasahar yada labarai da sadawa ta zamani, kuma nan da kasa da shekaru 10 muna so mu ga Najeriya a cikin kasashen da suka ci gaba ta fannin fasar yada labarai a duniya’’. In ji Dakta Olatunji

 

kazalika, Shugaban Hukumar ta NITDA ya bayyana cewar idan ana so a ga ci gaba ta fannin fasahar zamani, sai an mai da hanka akan kirkire-kirkire da kuma koyar da sanaóin hannu.

 

Abdulkarim Rabiu.