Nan bada jimawa ba za’a yi taron jin ra’ayin Jama’a kan kafa hukumar sake farfado da Arewa maso gabashin Najeriya.

Nan bada jimawa ba za’a gudanar da taron jin ra’ayin jama’a domin kafa hukumar sake farfado da Arewa maso gabashin Najeriya da rikin Boko Haram ya shafa, Sanata Ahmed Abubakar Mu’alliyidi mai wakiltar Adamawa ta kudu a majalisar dattawan Najeriya, shi ne ya bayyana hakan a zantawarsu da Muryar Najeriya dangane da ta’sar da rikicin Boko Haram din ya janyo a yankin da ma wasu sassa na Kasar baki daya.

“abun takaici kwarai matuka idan aka yi la’akari da dumbin rayuka da dukiyoyi da aka rasa sakamakon wannan balahira, a don haka, kafa hukumar na da fa’ida kwarai musamman idan aka yi la’akari da irin tasirin da hukumar Niger Delta ta yi a lokacin da yankin ya shiga tsaka mai wuya’’. In ji Sanata Mu’alliyidi

Kazalika, Sanatan ya yi karin haske dangane da rawar da su karan kansu ‘yan majalisun yankin ke takawa domin ganin sun ceto al’umarsu daga cikin ukubar da suka sami kansu, a inda yace suna gudanar da taro lokaci lokaci domin lalubo bakin zaren.

Sanata Mu’alliyidi ya yabawa shugaba Buhari da dakarun tsaron Najeriya kan irin namijin kokarin da suke yi domin ganin an kakkabe sauran ‘yan ta’addan da suka rage.

Ya kuma shawarci matasa da sauran mutanen yankin da su guji duk wasu sabbin dabarun da ‘yan ta’addan ke bullo da su domin ganin sun dulmiyar da su a wannan mummunar hanya, ciki kuwa har da bada bashin makudan kudade ga al’umma inda daga bisani su kan yi amfani da damar wajen ganin sun tursasa masu shiga kungiyar ta Boko Haram.

A karshe Sanata Abubakar ya yi amfani da wannan dama wajen yin addu’a ga Najeriya da Nahiyar Afirika da ma duniya baki daya domin kaucewa afkuwar irin wadannan tashe tashen hankula nan gaba.

Abdulkarim Rabiu/Musa Aminu