NLC ta dakatar da yajin aiki a Nigeria

Kungiyar kwadago ta kasa a Najeriya NLC, ta dakatar da yajin aikin gama gari da ta shiga.

A wani taro na majalisar koli da ta gudanar ranar lahadi a Abuja ne Kungiyar NLC ta yanke hukuncin janye yajin aikin da ya biyo bayan janye tallafin man fetur.

NLC dai ta shiga yajin aikin ne a ranar Larabar da ta gabata, domin nuna rashin amincewa da karin kudin man fetur da na latarki da gwamnati ta yi a kasar.

 

Daga cikin dalilan da ya kai NLC ga daukar wannan mataki, har da ganawa da daya daga cikin kusoshin jam’iyyar APC da ke mulki Bola Tinubu, wanda ya ba ta tabbacin tattaunawa da gwamnatin Najeriya kan janye tallafin man fetur.

 

Amma kungiyar kwadagon ta ce za ta ci gaba da tattauna ne kan matsayinta na cewa man fetur ya koma kan Naira 86 da Kobo 40 kowane lita, maimakon Naira 145. Amma za ta tattauna ne ba tare da yajin aiki ba.

 

Ana fatan kungiyar za ta koma kan teburin tattaunawa da gwamnati domin daidaitawa.

 

Abdulkarim Rabiu