NOA ta bukaci yin amfani da kayan da ake samarwa a Najeriya

Hukumar wayar da kan jama’a ta kasa a Najeriya NOA ta yi kira ga al’ummar kasar da ta rika sayan kayan da ake kera wa a Najeriya, domin taimaka wa bunkasar tattalin arzikin kasar.

 

Daraktan Hukumar na Jihar Kano dake arewa maso yammacin Kasar, Mohammed Bashir Ali, ya ce ko wane sashe na hukumar zai gudanar da gamgamin wayar da kan jamáa akan sayan kayan da ake samarwa a Najeriya.

 

Ya ce lokaci ya yi da ‘yan Najeriya zasu lura da halin da tattalin arzikin kasar yake ciki kana su sauya dabiínsu na sayar kayyakin da ake kera wa daga kasashen waje.

 

‘’ Hukumar NOA ta jihar Kano zata yi amfani da dukkan rassanta daga kasa zuwa sama, da ma’aikatanta wajen wayar da kan al’ummar Najeriya agame da rungumar kayayyakin da ake samarwa, a kowane lungu da sako na kasar’’. Daraktan Humumar na jihar Kano ja jaddada haka.

 

Ya kara da cewar Allah ya albarkaci Najeriya da albarkatun kasa masu yawa da zata iya dogaro da kanta da ma fitar da su kasashen waje.

 

Kazalika ya jaddada cewa gaggamin wayar da kan jamaar zai taimaka wajen cusa wa jama’a ra’ayin sayan kayan da ake samarwa a Najeriya da kuma bunkasa hayyoyin kudaden shiga don ci gaban kasar.

 

 

Abdulkarim Rabiu.