NOUN ta bukaci ‘yan Najeriya suka rika zuwa jami’ar domin karo karatu

An shawarci ma’aikatan gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu gami da wadanda Allah ya jarabta da nakasa ko tawaya da su rungumi akidar nan ta gemu baya hana ilimi, wato komawa makaranta domin kara ilimi ko da kuwa shekarunsu sun ja.

Wannan shawarar ta fito ne daga bakin shugaban jami’ar jeka ka dawo da ake koyan karatu daga nesa wato National Open University of Nigeria (NOUN) a turance, Farfessa Abubakar Garba Sulieman, inda ya bukaci hakan a lokacin da yake zantawa da Muryar Najeriya a ofishinsa dake harabar makarantar a unguwar Kubwa dake Abuja babban birnin tarayyar Najeriya.

Sheihin malamin yace cibiyar da yake jagoranta kadai nada dalibai sama da dubu hamsin, kana suna da irin wadannan cibiyoyin sama da hamsin a fadin kasar.

‘’ ina mai alfaharin sanar da masu sauraro cewa, yaye daliban da NOUN ta yi kwanannan, akwai wata gurguwa da ta gama da digiri mai daraja ta daya wato First Class Degree a jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya” in ji Farfessa Sulieman

Ya kara da cewar ko wace shekara baya ga fararen hula jama’iar na yaye jami’an sojoji, da ‘yan sanda da na hukumar kula da shige da fice da sauran jamain da ke sa kayan sarki.

Bugu da kari, ya ce kashi hamsin cikin dari na masu sha’awar shiga jami’oi kan sami guraben karatu a NOUN ne kadai, domin a cewarsa jami’oin kasar basu da isassun guraben da za su iya daukar ilahirinsu, a don haka ya mika kokon bararsa ga gwamnatin tarayya da data sake inganta jamaiar mai kowarwa da ga nesa.

Musa Aminu/Abdulkarim Rabiu