NUJ ta ware kwanaki 7 don nuna alhinin mutuwar tsohon shugabanta.

Kungiyar ‘yanjaridu ta kasa reshen Babban birnin tarayya ta ware kwanaki 7 domin nuna alhinin rasuwar tsohon shugabanta, Kwamared Chuks Ehirim.

A wata sanarwa da shugaban Kungiyar reshen Abuja, Kwamared Paul Ella, da sakatariyar kungiyar, Rafat Salami, suka fitar, ta bayyana marigayi Ehirim a matsayin “ gogaggen danjarida da ya shafe fiye da shekaru talatin ya na aikin jarida”.

Kwamared Ehirin wanda ya rigamu gidan gaskiya a ranar 16 ga watan Yuni da kuma ta yi daidai da ranar cikarsa shekaru 50 da haihuwa, ya yi shugabancin kungiyar ‘yanjaridu ta kasa reshen babban birnin tarayya Abuja a tsakanin shekarar 2012 da 2015.

“za a rika tunawa da marigayin a matsayin danjarida mara tsoro wanda ya yi amfani da aikinsa wajen kare martabar dimokuradiyya, kuma mutum ne mai rajin yancin kai da kuma gaskiya da adalci”.

” Za a rika tunawa da shi musamman a matsayin mutumin da ba ruwansa da banbancin addini ko kabilanci, wanda ya yi imani da hadin kan kasa, kuma a koda yaushe yake bata fifiko.” A cewar sanarwar.

Daga cikin abubuwan da kungiyar ‘yanjaridun zata gudanar yayin jimamin mutuwar tasa, an bukaci ko wane danjarida da ya sanya hannu akan rijistar ta’aziyyar a sakatariyar kunigyar dake unguwar Utako, da kuma sanya bakin tufafi a iya tsawon lokacin jimamin na kwanaki 7.

Har-ila-yau kungiyar ta bukaci mambobinta dake amfani da shafukan sada zumunta na intanet da “su yi amfani da hotonsa a matsayin (Frofile Picture) din su, sannan idan zasu yi sharhi su rika tuna wa da Chuks Ehirim”.

“ Mun bukaci hakan yayin da kungiyar take shirin yin wani taron gangami na kaddamar da gidauniyar Naira Miliyan 100 don tallafawa ilimin kanana yara da kuma wani taron lakca akan Marigayin, wanda aka yi wa lakabi da ‘taron lakca na Chuks Ehirim’, domin wayar da kan jama’a akan mahimancin aikin jarida da kuma bukatar dake akwai ta kare ‘yanjaridu daga ayyukan bauta, da kuma cin zarafinsu da wasu kafafan yada labarai ke yi, lamarin da marigayi Chuks Ehirin ya taba tsintar kansa a ciki alokacin yana raye”.

Kwanaki bakewan na nuna alhini ga rasuwan Kwamared Chuks Ehirim za su kare ne a wani babban taro da kungiyar ‘yanjaridun ta shiryya gudanarwa a ranar 25 ga watan Yuni.

Abdulkarim Rabiu