Red Cross ta sake hada kan iyalai 23 a arewa maso gabashin Najeriya.

Kungiyar bayar da agaji ta kasa da kasa (Red Cross), ta ce ta sake hada kan iyalai 23 wadanda suka daidaice a sanadiyyar rikicin Boko Haram a yakin arewa maso gashin Najeriya.

Shugaban wani bangare na wakilan kungiyar, San Roman ne ya bayyana hakan a garin Yola a wata hira da maneman labarai.

San roman ya ce an sake haka kai iyalan ne biyo bayan tunbubar da kungiyar ta rinka yi ta wayar tarho da tattara hotuna da kuma yin amfani sauran hanyoyi na neman bayanai.

kawo yanzu mun samu nasarar sake hada kan iyalai 23 daga yankin arewa maso gabashin Najeriya wadanda suka daidaice kuma suka rabu da ‘yan uwansu a dalilin rikicin Boko Haram.

“daga cikin su kuma akwai wadanda suka tsallaka kan iyakoki’’ In ji San Roman.

Har-ila-yau ya bayyana cewar daga cikin iyalai uku da suka tsallaka kan iyaka sun hada da wadan ya fito daga kasar Chadi da kuma wasu biyu daga kasar Kamaru.

San Roman ya kara da cewa an bullo da shirin ne da nufi taikamaka wa iyaye ko kuma ya’yan da suka bace wadanda ka iya shiga wani mummunan mawuyacin halin rayuwa.

Ya ce nan bada jimawa ba kungiyar za ta kara shirya wani shirin na sake hada kan iyalai da suka fito daga kasashen Chadi, da Niger, da kuma Kamaru.

 

 

Abdulkarim Rabiu.