Rundunar sojin Najeriya ta kara ceto wata daga cikin yan matan chibok

 

Rundunar sojin Najeriya tare da hadin kan yan kato da gora sun sami nasarar kara ceBo wata daga cikin yan matan makaratar Sakandaren Chibok da yan boko Haram suka sace a ranar 14 ga watan Afrilu.

Mai Magana da yawun rundunar sojin kanal Sani Usman kuka a wata sanarwa ya bayyana cewa ’’an yi Imani da cewar yarinyar mai suna Serah Luka yar wani fasto ce kuma itace ta 157 a cikin jerin sunanyen yan matan Chibok da yan Boko haram suka sace, sannan yar asalin garin Madagali ce dake jihar Adamawa a yankin arewa masu gashin Najeriya’’.

Kanal sani Usman kuka ya kara da cewa dakarun sun kuma yi nasarar kasahe yan Boko Haram 35 kana sun kwace manyan Makamai da alburusai.

A cewar mai Magana da yawun rundunar Sojin Najeriyar mata 97 ne yan Boko haram din suke tsare da kuma sun sami yancin kansu a lokacin da sojojin suka kai sumamen.

Yanzu hakan yarinyar da sojojin suka ceto na samun kulawa a asibitin barikinn sojoji na Abogo Largema a karamar hukmar biu dake jihara Born a arewa maso gasahion Najeriya.

 

Abdulkarim Rabiu