Rundunar sojin Najeriya ta yi wani sunturi na sharar daji a

A wani yunkuri na samar da tsaro da bude hanyoyin mota a jihar Borno, dakarun Najeriya da tare da ‘yan sunturi ko kuma yan kato da gora sun gudanar da  wani sunturi na sharar daji daga kauyen Bitta zuwa hanyar data hada kauyen Gambori dake Jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya.

Mukaddashin daraktan hurda da jama’a na rundunar sojin Najeriya Kanal Sani Usman Kukasheka, wanda ya bayyana hakan, yace “a lokacin sunturin, dakarun Najeriya sun yi artabu  da ‘yan Boko Haram a kauyen Bulajani kuma sun yi nasarar tarwatsasu.

Sai, dai daga bisani an yi wa dakarun kwanton bauna, dalilin da ya sa kenan suka ja da baya. Sojoji 5 sun sami raunika kuma an latata motarsu ta yaki, yayin da sojojin suka sami nasarar kashe ‘Yan Boko Haram 4, a inda dama suka tsere da raunika a jikinsu.

Sojojin sun kuma sami nasarar kwace kekune 6 da kayyakin abinci. Kazalika sun sami nasarar warware wani bom a kauyen Madube.

’’ tuni dai aka kai sojin da suka sami raunika zuwa asibitin sojoji dake garin Yola domin samun kulawa’’ in ji kanal Usman

A wani labarin kuma wata tawagar dakarun Najeriya da ‘yan kato da gora ko kuma (Civilian JTF) sun gudanar da wani sunturi a kauyen Albanya da kewayensa.

’’ dakarun sun yi bata kashi da yan Boko Haram a kauyen Sinabaya dake hagu da titin da ya toso daga Marte zuwa Kaje a karamar hukumar Dikwa dake Jihar Borno. A lokacin sunturin, dakarun sun kashe Yan Boko Haram 3 yayin da suka sami nasarar kama 11’’.

Har-ila-yau tawagar sunturin ta sami nasarar gano bindiga samfurin AK-47 da aka yi wa rijista N37113 da kuma bindigogi 5 masu aman wuta. Sauran kayan da a samu sun hada da gurneti 36, alburusai 3, motoci 4, da kekune 3, da jaka da kuma wayar salula guda daya.

 

Abdulkarim Rabiu.