Shugaba Buhari ya yaba wa goyon bayan Amurka a zaben 2015

Sanusi Lamido

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana godiyarsa dangane da mahimmiyar rawar da gwamnatin Amurka ta taka wajen samun nasarar babban zaben Najeriya na 2015.

 

Da yake karbar bakuncin jakadan Amurka mai barin gado Mista James Estwistle, a fadarsa, shugaba Buhari ya ce dagewar da Amurka ta yi kan sai an gudanar da zabe cikin gaskiya da adalci wanda kuma babu ruwansa da tashe-tashen hankula ya taimaka mutuka wajen karfafa mulkin dimokuradiyya a Najeriya.

 

’’Goyon bayan da Amurka ta bayar kafin zaben 2015 da lokacin da ake yi da  kuma bayan an kammala ya taimaka mutuka wajen daidaituwar al’amura a Najeriya, saboda haka bazan taba manta gudun mawar da suka bayar wajen daidaituwar al’amura a Najeriya ba, mun yi sa’a muna da shugaban hukumar zabe wanda ya cancanta kuma mai karfin hali da juriya’’  In ji Shugaba Buhari

 

Shugaban na Najeriya ya ce ’’ambasada ka sami mukami adaidai lokacin da Najeriya  ta kafa tahiri, kuma ina fata masana tarihi zasu aje wannan, saboda yana da matukar mahimmacin ga daidaituwar al’amuran Najeriya. Ina fata zaka rubutata littafi dangane da abubuwan da ka ganewa idanunka a Najeriya. Goyan bayan da Amurka ta bai wa Najeriya ba zai iya musaltuwa ba.’’

 

 

Abdulkarim Rabiu.