Shugaba Buhari Ya Yi Tur da Yunkurin Juyin Mulki a Turkiyya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bi sahun takawaransa na Amurka Barack Obama da sauran shugananin kasashen duniya wajen yin Allaha wadai da yunkucin juyin mulkin da bai yi nasara ba a kasar Turkiyya, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar fiye da mutane 100.

 

Da yake maida martini agame da yunkurin juyin mulkin, shugaba Buhari ya ce ’’ya ji takaici da ya sami rahoton yunkurin juyin mulkin da zai dagula zababbiyar gwamnatin dimokuradiyyar Shugaba Tayyip Erdogan na kasar Turkiyya.

 

’’ba za a kara yadda da kifar da gwamnatin dimokuradiyya da karfin soji ba. Tashin hankali ba zai taba kawo masalaha ga matsala ba, sai ma dai ya kara tabarbara al’amura da ci gaban mulkin dimokuradiyyar al’umma.’’

 

Shugaban na Najeriya ya kuma bayyana Shugaba Erdogan a matsayin aminin Najeriya kuma mai goyon bayan shirin yaki da ta’addancin da yanzu haka Najeriya take yi.

 

Shugaban ya kuma ya yabawa karfin gwiwa da kuma kokarin da fararen hular kasar suka nuna wajen maida da martini tare da fatttakar ‘yantawayen masu dauke da bindigogi da suka yi yunkurin kifar da gwamnatin.

 

Kazalika shugaba Buhari ya yi kira ga shugaban Turkiyya da ya nemi sulhu a tsakaninsa da yantawen, kana ya bayyana cewa Najeriya a shirye take ta bayar da goyan bayanta ga gwamnati da al’ummar Turkiyya a lokacin da suke fama da tashe-tashen hankula.

 

Abdulkarim Rabiu.