shugaba Buhari yana gana wa da ministoci kan kasafin kudi na 2016

Yanzu haka dai majalisar zartarwar Najeriya ta gudanar da taro a fadar shugaban kasa dake Abuja babban birnin kasar.
An dai fara taron ne da misalin karfe 10:00 na safe agogon GMT karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari.
Taron zai maida hankali ne kan nazarin cikakkun bayanan kasafin kudi na 2016 domin shugaba Buhari ya amince da shi.
Taron dai ya samu halartar mataimakin shugaban Najeriya, yemi Osinbajo, da Sakataren gwamnatin tarayya, da shugaban ma’aikatan gwamnati da kuma ministocin kasar baki daya.
Nan gaba kadan za a ji Karin bayani bayan an gabatarwa da manema labarai cikkakkun bayani a karshen taron.

Abdulkarim Rabiu