Shugaba Buhari Zai kaddamar da layin dogo na Abuja zuwa Kaduna.

A farkon makon watan Yulin 2016 ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai kaddamar da titin jirgin kasa da aka kammala aikinsa wanda ya tafi daga Abuja zuwa kaduna da ya lakume zunzuruntin kudi har Dala Miliyan dubu daya.

Ministan sufuri, Rotimi Amaechi ne ya bayyana hakan a Abuja babban birnin kasar yayin da yake rangadin gwaji zuwa garin kaduna dake yankin arewa maso yammacin kasar, inda ya jaddada cewa idan aka kaddamar da layin dogon, za a bukaci fasinjoji su mallaki kadin shaidar zama dan kasa ko kuma ko wane irin katin shaidar aikin yi.

abin da na gani yau ya bani mamaki kuma dole ne ince aiki ya yi, dalilin da yasa ba zamu fara aiki ba shi ne wajibi ne mu yi laákari da hakkin da ya rataya akan shugaba Muhammadu Buhari na kaddamar da jirgin, wanda kuma ana sa ran haka nan da zuwa makon farko na watan Yuli” In ji Minista.

Minstan sufurin ya kara da cewa, “za a yi amfani da makonnin biyun farkon watan Yuni don yin gwajin jiragen kasan  ba tare da daukar fasinjoji ba, yayin da sauran makonnin biyu za a yi gwajin tare da fasinjo kuma kyauta. Muna sa ran nan da zuwa makon farko na watan Yuli shugaban kasa zai kaddamar da layin dogon, mun yi imani da cewa shugaban Buhari zai kaddamar da shirin, daga nan kuma duk wanda zai shiga sai ya biya.”

Tun da fari an bayar da kwantiragin ginin layin dogon akan dala miliyan 849,000, amma mun yi amfani da dala biliyan daya da milyan hudu sabo da an hada da ginin katange layin dogon daga garin Abuja zuwa kaduna ta ko wane bangare domin kare dabbobi da biladama daga tsallakawa.

Da yake bayani agame da yin amfani da katin shaidar dan kasa yace zamu yi amfani da katin shaidar dan kasa saboda tsaro. Muna so mu san masu shiga jirgin ‘kasan da kuma wadan da ba za su shiga ba. Dole ne su sami katin shaida.

 

 

Abdulkarim Rabiu