Shugaban Masar ya gargadi masu zanga-zangar adawa

A ranar Litinin ne ‘yan kasar Masar ke yin babbar zanga-zangar nuna adawa da gwamnati dangane da mika wasu tsibirai ga Saudiyya.

Gabanin babban gangamin dai, shugaban kasar Abdulfatah Al Sisi ya yi kira ga jama’ar kasar su kare kasarsu.

Shugaba Al Sisi ya ce duk wani yunkuri na raba kan al’ummar kasar ba zai yi nasara ba idan jam’a suka hada kansu.

Ana dai samun karuwar kosawar jama’a da gwamnatin Masar tun bayan yarjejeniyar da ta mika wasu tsibirai ga Saudiyya.

Batun mika tsibiran dai na ci gaba da zama babban batu da ke janyo adawa ga gwamnati a Masar.

A wani labarin kuma, shugaba Al sisi ya gargadi agame da zanga-zangar da ya kira yunkurin tarwatsa kasar.

Adbulkarim Rabiu