Shugaban Muryar Najeriya ya bukaci kabilar Igbo ta mara shugaba Buhari baya.

Babban daraktan gidan radiyon Murayar Najeriya, Mr. Osita Okechukwu ya bukaci al’umar yakin kudu maso gabashin kasar da ta hada hannu da shugaba Muhammadu Buhari a yakin da yake yi da cin hanci.

Ya ce babbar matsalar da ke addabar Najeriya shi ne kwadayi, wanda kuma shi ke haifar da cin hanci da rashawa.

“kamata ya yi mu hada hannu da shugaba Buhari wajen yaki da cin hanci da kuma rashin tsaro. kalubalen tsaro da suka hada da rikicin Boko Haram da masu satar mutane domin neman kudin fansa da yanzu haka Najeriya take fuskanta ya samo asali ne daga cin hanci da rashawa. Idan muka yaki cin hanci za mu samu kasa mai albarka.” Ya fadi hakan ne a wajen wata liyafar karrama shi da aka gudanar a Jihar Enugu.

Shugaban gidan radiyon Muryar Najeriyar ya kara da cewa Allah ya albarkaci Najeriya da yawan al’umma da kuma albarkatun karkashin kasa wadanda za su ishi kowa ’’ sai dai saboda kwadi wasu tsiru ne kawai suke amfana da su wanda a sanadiyyar hakan ya bar kusan kashi 80 bisa 100 cikin talauci.’’

Ya ce sam-sam bai yadda da banbancin addini ko kabilanci shi ne matsalar da ke addabar ci gaban Najeriya ba.
Shugaban ya bayar da misali da garinsa, Eke wanda kusan duka al’ummarsa kabilar Igbo ce dake amfani da harshe iri daya kana kashi 99 bisa 100 Kiristoci ne mabiya darikar Katolika, amma duk da haka ana samun banbanci a tsakaninsu.

Har-ila-yau ya yi kira ga wadanda ke neman a raba Najeriya da su yi watsi da wannan batu kana su mara wa shugaba Buhari baya domin ciyar da Kasar gaba.

Da yake na sa jawabin shugaban kungiyar ci gaban al’ummar garin Eke, Farfessa Bartho Okolo, ya bayyana karfin gwiwarsa kan sabbin shugabannin za su sauke nauyin da ya rataya akansu yadda ya kamata.

An dai karrama shugaban gidan radiyon Muryar Najeriya da Ministan harkokin wajen Najeriya Dr. Geoffrey Onyeama a wata liyafar cin abinci da aka gudanar a garin Eke dake karamar Hukumar Udi a jihar Enugu.
Shi ma da yake nasa jawabin gwamna Ifeanyi Ugwuanyi ya mika godiyarsa ga shugaba Muhammadu Buhari da ya bai wa Onyeama da Okechukwu wadannan mahimman mukamai.

Kazalika ya bukaci da su kasance jakadun jihar nagari kana su jajirce wajen gudanar da aikin da ya rataya akansu.

Abdulkarim Rabiu.