Shugaban Najeriya ya sha alwashin kare bututan mai dake yankin Naija Delta.

Shugaba Buhari ya tabbatar wa al’ummar Najeriya cewa za yi iyakar kokarinsa ya kare bututan mai da saurar kadarorin gwamnati dake yankin Naija Delta.

Shugaba Buhari ya bayar da tabbacin hakan ne yayin da yake gabatar da jawabi a wani taron lanca na tunawa da ranar Dimokuradiyya wanda kungiyar dake rajin kare mulkin dimokuradiyya ta Afrika ta shirya a garin Abuja babban birnin kasar domin bikin tunawa da ranar dimokuradiyya ta shekara ta 2016.

Taken taron laccar shi ne Ajandar sauyi da ci gaban Dimokuradiyyar Najeriya.

Shugaban kasar wanda sakataren gwamnatin tarayya Babachir David Lawal ya wakilta, yace gwamnati ba zata yi kasa a gwiwa ba wajen nemo masalaha akan matsalar fasa bututan mai a cikin kasar ba.

“zaku yarda da ni kan cewar manyan dalilai guda biyu da suka yi sanadiddayar  tattalin arzikinmu ya shiga wani mummunan hali na tabarbarewa shi ne faduwar fashin danyen mai a kasuwar duniya.”

’’Har ila yau har da raguwadar yawan man da ake hakowa saboda hare-haren da ‘yan tawaye ke kai wa kwananna akan bututan mai dake yankin Naija Delta mai arzikin man fetur.’’

“yayin da  alhakin kayyade farashin man ba ya hannumu, hakimmu ne mu dauki makatai akan ayyukan yantawe da suke fasa mututan mai.

“saboda haka ina kara jaddada cewa na bai wa dukkan hukumomin tsaro da suke da ruwa da tsaki da su dauki matakan da suka wajaba domin kare bututan mai da kadarorin gwamnati dake yankin Naija Delta.

“yayin da kofofinmu a bude suke domin tattauna wa, agame da hanyoyin sulhu akan batun ba tare da daukar matakin soji ba, gwamnati ba zata yi kasa a gwiwa ba wajen kare al’ummar kasar daga shiga mummunan mawuyacin halin rayuwa ba’’.

Kazalika, ya bukaci yan tawayen da su guji wannan aika-aika ko kuma su fuskanci fushin hukuma.

 

Abdulakrim  Rabiu.