Shugabar Brazil ta dauka kara agame da yunkurin tsigeta

A kasar Brazil a wannan Laraba ce ‘yan majalisar dattawan kasar ke bayyana matsayinsu kan shirin tsige shugabar kasar Dilma Rousseff daga kan kujerar shugabanci, lamarin da zai kasance tsani na karshe ga samun hurumin gurfanar da ita a gaban kuliya domin aiwatar da matakin a bisa zargin cin hanci.

 

Ana dai kyautata zaton ‘yan majalisar dattawan za su kada kuri’ar amincewa da matakin gurfanar da shugabar a gaban kotun don tun kafin kai wa ga zaben, kimanin 50 daga cikin 81 na ‘yan majalisar sun bayyana goyon bayansu ga shirin.

 

A yammacin jiya Talata dai Shugaba Rousseff ta yi wani yinkurin karshe na neman dakatar da wannan shiri ta hanyar shigar da kara a gaban babbar kotun kolin kasar inda ta bukaci da ta dakatar da abin da ta kira juyin mulki.

 

Idan har ‘yan majalisar dattawan suka amince da matakin, to nan take za a dakatar da shugabancin Rousseff har na tsawon kwanaki 180 kafin bayyana sakamakon shari’ar tsigeta daga kan kujerar mulkin a watan Satumba mai zuwa.

 

A wani labarin, kuma Shugaba, Dilma Rouseff ta bukaci kotun ƙolin kasar ta dakatar da yunƙurin tsigeta.

 

Wannan dai matakin karshe ne na katse shirin yin kuri’a a majalisar dattawa dangane da batun.

 

Shugabar ta Brazil dake fama da fadi tashin siyasa, ta musanta zargin da ake yi mata na yin amfani da kasafin kudi lokacin zaɓe.

 

Idan dai har wasu daga cikin ‘yan majalisar dattawan suka jefa kuri’ar amincewa da yunkirin tsige shugabar, to hakan zai bude kofar soma shirin tsige ta, a ranar Larabar nan.

 

Abdulkarim Rabiu