Shugabar Ma’aikatan gwamnatin Tarayya ta sha alwashin farfado da Kulub din ma’aikata

Shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayyar Najeriya, Mrs Winifred Oyo-Ita ta ce yanzu haka ana nan ana kokarin farfado da Kulub din ma’aikatan gwamnti ko kuma wurin shakatawa, domin ma’aikatan su ci gajiyar wurin.

Uwargida oyo-Ita ta bayyana hakan ne yayin da take zantawa da kafanin dillacin Labarai na Najeriya( NAN) a Abuja babban birnin kasar, bayan ta kai ziyarar gani da ido a wurin.

Ta ce ya zama wajibi a farfado da kulub din wanda aka kaddamar shekaru 16 da suka gabata karkashin jagorancin tsohon sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya Dakta Gidado Idris.
Har-wa-yau shugaban Ma’aikatan Gwamnatin tararrayar t ace akwai bukatar farfado da kulub din ganin irin ababen more rayuwar da suke yanzu haka a wurin.

“ kalli filin wanda ke da mutukar daraja a unguwar Mabushi ya dade ba a amfani da shi.
“ ba zan yadda a bar wurin nan da aka kashe kudi ya lallace kamar haka.
“ an kafa wani kwamiti karkashin jagorancin sakataren dundundun na hukumar domin ya gabatar da shawarwari akan yadda za a farfado da Kulub din”
“ Mun ga wasu mutane da ba mu san ko su wane ne ba, suna zaune a wurin, kana wasu kuma sun mamaye wani bangare na filin “ a cewarta.

Oyo-Ita tace ofishinta zai gayyaci hukumomin kasar domin su gudanar da bincike agame da wadan da suka mamaye wani bangare na wurin, kuma za a kai rahoto ga yansanda.

Abdukarim Rabiu