Somalia: Wani tsohon dan majalisa ya tsallake rijiya da baya

Wani Tshohon dan majalisar dokokin Somaliya Yusuf Ayte ya tsallake rijiya da baya bayan da aka yi yunkurin hallaka shi yayinda bama-bama da aka dana a motarsa suka ta shi a Mogadishu babban birnin kasar.

Tshon dan majalisar dai baya kusa da abin hawansa a lokacin da bashewar ta auku a kusa da Otel din Wehliye, lamaran da ya sa kenan ya tsallake rigiya da bayan.

Wata kafar yada labarai ta kasar ta rawaito cewa Hukumar liken asirin Somaliya ta gano inda aka aje motar mai dauke da abubuwa masu mashewa.

Kawo yanzu babu wani Karin bayani agame da wadanda suka dauki alhakin kai wannan hari akan tsohon dan majalisar, wanda kuma malamin addinin Muslunci ne. koda yake dai kasar na fama da hare-haren kungiyar Alshabab wadda ta dade tana kai hare-hare makamantan wannan.

Tun dai a karshen watan jiya ne kungiyar ta kai wani hari a wani Otel dake babban birnin kasar wanda kuma ya yi sanadiyyar kisan mutane 15 a cewar jami’an ‘yansanda. Daga cikin wadanda suka mutu sakamakon harin harda karamin Ministan Muhalli Buri M. Hamza.

Har-wa-yau ‘yansandan sun bayyana cewa an fara kai harin ne da kunar bakin wake kafin daga bisani kuma a ci gaban da harbe-harben bindiga.

Tuni dai kungiyar Alshabab take musayar wuta da dakarun Somaliya da na Kunyiyar Tarayyar Afrika.

Abdulkarim Rabiu.