Uwargidan shugaba Buhari ta bukaci hadin kai wajen yaki da safarar miyagun kwayoyi.

Mai dakin shugaban Najeriya, Aishatu Buhari ta ce wajibe ne a hada hannu da gwamnati da sauran dukkan masu ruwa da tsaki wajen  yaki da safarar miyagun kwayoyi da laifukan makamantan wannan a cikin kasar.

 

Wata sanarwa da ta fito daga ofishin mai bai wa uwargidan shugaban kasa shawara kan harkokin yada labrai Zakari Nadabo, ta bayyana cewar ta bayar da shawarar ne a sakonta na bikin yaki da sha da kuma fataucin miyagun kwayoyi na kasa da kasa.

 

Uwargidan shugaban kasar ta jaddada kudirinta na ci gaba da wayar da kan ‘yan Najeriya akan illar sha ko fataucin miyagun kwayoyi, musamman a tsakanin yara da ka iya fuskantar barazanar fadawa mawuyacin hali.

 

Tace shirinta na tallafawa masu karamin karfi zai maida hankali ne wajen bunkasa rayuwar iyaye mata da yara kanana wadanda sune suka fi rauni a cikin alúmma.

 

Uwragidan shugaban kasar ta bayyana cewa ‘’ya kamata iyaye su jajirce a ko wane lokaci, su rika lura da yaransu da abin dake faruwa a unguwannisu domin kaucewa tsunduma cikin mawuyacin hali da zai lallata rayuwar yayansu.’’

 

Kazalika mai dakin shugaban kasar ta yaba wa Majalisar dinkin duniya dangane da irin tallafin data ke bai yara kanana da kuma batutuwan da suka shafi yaki da miyagun kwayoyi, domin hakan zai taimaka wajen cimma burin da ake bukata.

 

Abdulkarim Rabiu