VON zata hada hannu da NOA da kuma ma’iakatar harkokin waje akan yada labarai

Babban daraktan Muryar Najeriya VON, Mr. Osita Okechukwu ya ce a matsayin gidan radiyo na kasa da kasa zai hada hannu da ma’aikatar kula da harkokin wajen Najeriya da kuma hukumar wayar da kan jama’a NOA domin sanar da masu sauraro daga kasashen ketare da kuma jami’an diflomasiyya akan ayyukan hukumar wayar da kan jama’a da kuma irin sauye-sauyen da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari yanzu haka take kan yi.

Mr. Okechukwu ya bayyana hakan ne a lokacin da tawagar jami’an gudanarwar Hukumar wayar da kan jama’a karkashin jagorancin babban daraktan hukumar Dakta  Garba Abari suka kai ziyarar aiki a ofishinsa dake Abuja babban birnin kasar.

Har-wa-yau ya bayyana irin damarmakin da hukumar wayar da kan jama’ar take da shi, inda ya bukace su da su yi amfani da wadannan damarmaki wajen yi wa jama’a da gwamnati aikin da ya dace. Yace Muryar Najeriya a shirye take ta yi aiki da hukumar NOA.

’’Hukumar wayar dakan jama’a ta cancanci hadin gwiwa. A don haka, zan bada shawara mu kafa wani kwamiti domin hada gwiwa da maáikatar harkokin wajen Najeriya, da hukumar wajen da kan jama’a da kuma Muryar Najeriya, domin samun kyakyawar alaka a tsakaninmu yayin da kuma za mu rika amfani da kafarmu wajen yada labarai ga masu sauraren mu a kasashen ketare da kuma jami’an diflomasiyya agame da abin da Najeriya take ciki, da manufofi da shriye-shiryen gwamnati na ci gaba.’’ In ji Mr Okechukwu.

Yace wajibi ne tuninin masu saurerenmu a kasashen waje da yan Najeriya ya sauya akan wasu batutuwa da suka shafi harkokin gwamnati. Kuma anan ne hukumar wayar da kan jama’a zata bayar da gudun mawarta tare da hadin gwiwar Muryar Nigeriya, wanda shi ne  gidan radiyon Najeriya na kasa da kasa da yake yada shirye-shiryensa a cikin harsuna 8.

Da yake nasa jawabin, babban daraktan hukumar wayar da kan jama’a Dakta. Garba Abari yace hukumar tana da kyakkyawan tsari da zai isar da sakonni ga al’ummar Najeriya.

Kazalika, ya bukaci ma’aikatu da sashe-sashe na gwamnatin tarayya da su yi amfani da hukumar wayar da kan jama’a wajen isar da sako ga alumma.

Ya ce hukumar zata bude wani dandalin sada zumunta na yanar gizo inda ‘yan Najeriya za su sami damar bayar da gudun mawarsu akan irin ayyukan da hukumar take yi.

Har-ila-yau ya bukaci Muryar Najeriya ta taimakawa hukuamar wayar da kan jama’a wajen yada shirye-shiryenta ga dubbun masu saurare a cikin harsuna takwas da gidan radiyon yake watsa shirye-shiryensa.

 

Abdulkarim Rabiu.