WHO zata maida hankali kan fannin kiwon lafiya a matakin farko na Najeriya

Daraktar kula da yankin Afrika ta Hukumar lafiya ta duniya WHO, Dakta Matshidiso Moeti, ta fara zayarar aiki ta kwanaki uku a Najeriya.

 

Daraktan yankin wadda yanzu haka ta zo Najeriya a karo na biyu cikin shekara guda, ta ganawa da Ministan Lafiya da kuma shugabannin hukumimin dake karkashin ma’aikatar ta kiwon lafiya.

 

Dakta. Moet ta bayyana cewar ta yi mutukar murna da irin nasarar da fannin kiwon Lafiyar Najeriya ya samu.

 

Har-ila-yau ta bai wa Najeriya tabbacin cewar Hukumar Lafiya ta duniyar zata ci gaba da bai wa Najeriya goyan baya wajen bunkasa fannin kiwon lafiya.

 

‘’ yana da mutukar mahimmanci a gareni in san abin da kuka fi bai wa fifiko a bangaren kula da lafiya a matakin farko da kuma mataki na bai daya, saboda wannan shi ne abin da Hukumar Lafiya ta duniya ta sa agaba’’ In ji Dakta. Moet

 

Kazalika ta bukaci gwamnati ta karkafa gwiwar masu ruwa da tsaki a fannin kiwon lafiya domin su maida hankali a akan yankunan da aka gina asibitocin dake kula lafiya a matakin farko.

 

Abdulkarim Rabiu