Yau ne ake bukin ranar yaki da Maleriya ta duniya na 2016

A ranar Litinin ne ake bikin ranar yaki da cutar zazzabin cizon sauro, watau Malaria ta duniya.

Majalisar dinkin duniya ta ware ko wace ranar 25 ga watan Afrilun ko wace shekara ta zama ranar bikin yaki da zazzabin cizon sauro domin matsa kaimi wajen kawar da cutar.

Alkaluma sun yi nuni da cewar a kalla mutane 338,000 ne ke mutuwa duk shekara sanadiyyar kamuwa da cutar, sannan mutane miliyan 414 na kamuwa da cutar.

Kashi 90 cikin 100 na masu kamuwa da cutar a Nahiyar Afirka suke.

Mutane da dama ne ke fuskantar barazanar kamuwa da cutar a duniya muddin ba a dauki wani mataki ba.

Taken ranar ta bana dai shi ne ‘Kawo Karshen Maleriya don Samun Alheri’.

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO dai ta ce kasashen Turai sun cimma burin kawar da cutar zazzabin na cizon sauro tun a bara.

Amma har yanzu cutar na mummunar barna a kasashe masu tasowa.

Kasashen Afirka shida ne za su yi ban kwana da cutar Maleriya nan da shekarar 2020 kamar yadda rahoton Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ya nunar a ranar Litinin din nan, rahoton da ke fita a wani bangare na bikin ranar Maleriya ta duniya.

A cewar hukumar kasashe 21 ne ke da alamu na iya kawar da cutar ciki kuwa har da shida daga nahiyar Afirka.Wadannan kasashe kuwa su ne Aljeriya da Baswana da Cape Verde da Kwamaras da Afirka ta Kudu da Siwaziland.

 

Abdulkarim Rabiu