Yau take Sallah a janhuriyar Nijar

Buhari,Jonathan, Obasanjo

Rahotanni daga jamhuriyar Nijar na cewa a ranar Talatar nan ne Musulman kasar suke gudanar da bikin karamar Sallah, bayan ganin jaririn watan Shawwal a ranar Litinin.
Hakan dai ya biyo bayan sanarwar da firai ministan kasar, Briji Rafini, ya bayar, a daren Litinin cewa Talata ce daya ga watan Shawwal.
An dai ce jama’a sun ga jaririn watan ne a sassa da dama a fadin kasar.
Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da makwabciyar kasar wato Najeriya ta sanar da yin tata sallar, a ranar Laraba.

BBC/ Abdulkarim Rabiu