An bukaci dinlalan man fetur a Najeriya kada su fake da cire tallafi wajen gallazawa jamaa

An bukaci jagororin kungiyar dillalan man fetur a Najeriya da suji tsoron Allah a duk lokacin da suke gudunar da hada hadar kasuwancinsu kana kada su fake da cire tallafi kan albarkatun man fetur da gwamnatin tarayyar kasar ta yi domin gallazawa al’umma.

Wannnan bukata dai ta fito ne daga bakin tsohon ministan albarkatun man fefur din kasar, Alhaji Umaru Dembo a lokacin da ya ke zantawa da Muryar Najeriya da sanyin safiyar lahadin nan a gidansa dake cikin birnin Zariya jihar Kaduna dake yankin Arewa maso yammacin Najeriya.

Tsohon ministan a tarayyar Najeriya ya ce ba wai dillalan man fetur ba kadai ba, har ma ilahirin yan kasar musamman yan kasuwa da sauran masu sana’oin hannu ya zama wajibi su sauya dabi’un su domin samun waraka a tsakanin al’umma.

Umaru Dembo ya ci gaba da cewa lokaci ya yi da al’umar Najeriya za ta dukufa wajen addu’oi ga gwamnati mai ci domin neman alheri bisa manufufofin da ta sa a gaba, ba wai maganganun suka da batanci ba.

Dangane da batun cire tallafin kuwa, wanda da dama daga cikin yan Najeriya ke tofa albarkacin bakunan su a halin yanzu, tsohon ministan albarkatun man fetur din na da ra’yin cewa “Tallafi dai an ri ga ya an cire, abinda ya rage shi ne mu yan kasa mu yi addu’a Allah ya sa haka ya zama alheri ga Najeriya da kuma al’umman cikinta”

Da yake tofa albarkacin bakinsa dangane da batun ci tallafin mai kuwa, Alhaji Umaru Dembo yace ” ai dama Sallah daga liman take baci, yanzu dai ka ga mun sami jigo na kwarai a matsayin shugaba don haka bamu da tan tama kuma insha Allahu ba za a yi wani burun burun ba a harkar, mu dai mu dan kara hakuri muga ikon Allah.”

Kazalika, Dattijon ya yaba dan gane da yunkurin gwamanatin tarayya na sake bun kasa harkar noma da nufin rage dogaro akan albarkatun man fetur da Najeriya ta dade tana yi.

Abdulkarim Rabiu/ Musa Aminu Dambo.