An bukaci kwamitin rikon PDP ya sasanta rikicin da ke cikin jamiyyar.

Mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya Sanata Ike Ekwerenmadu, ya bukaci kwamitin rikon kwarya na Jamiyyar PDP da ya maida hanakali wajen sasanta rikicin dake cikin jam’iyyar.

Sanatan ya kuma bayyana kwarin guiwa ga cancanatar Shugabancin Sanata Ahmed Makarfi da tawagarsa.

Sanata Ekwerenmadu ya ce babu wani rashin halarci ko son rai  a taron kafa shugabannin riko na jammiyar ba, Sanatan ya ci gaba da cewa babu wani zabe da aka yi a taron face shuwagabannin jam’iyyar sun amfani  da karfin ikonsu na karfin fada a ji wajen kafa kwamitin na riko da zai gudanar da zabe cikin watanni uku.

Sanatan ya bayyana hakan ne a filin sauka da tashin jiragen sama na Nnamdi Abubakar dake Abuja babban birnin kasar, yayin da ya dawo daga birnin Fatakwal bayan ya halarci taron kafa kwamitin riko da jam’iyyar adawar ta gudanar.

Sanata Ekwerenmadu wanda ya rifawa Shugaban Kwamitin riko Sanata Ahmed Makarfi baya, ya ce abin da ke damun jamiyyar shi ne son rai wanda a cewarsa ko wace jamiyya tana fuskantar irin wannan matsala a tsakanin yayanta.

“Sanata Makarfi shugaba na gari, ne kuma mai kishin kasa kana mutum ne wanda na yi aiki da shi shekaru da yawa a majalisa. Ya bayar da gudunmawarsa a kwamitin bibiyar zaben jamiyyar PDP wanda na jagoranta, ina da tabbacin cewar shi da tawagarsa za su daidaiata rikicin dake cikin jam’iyyar kana su gudanar da sahihin zabe cikin gaskiya da adalci”. In ji sanata Ekerenmadu.

 

Daya bangaren Jamiyyar PDP

Mataimakin shugaban majalisar dattawan ta Najeriya, ya kuma yi watsi da rahotannin da suka yi nuni da cewar an sami rarrabuwar kai a jamiiyar ta PDP inda wani bangaren ya yi ikirarin kafa shugabancin jam’iyyar.

“kamar yadda nake fada babu wani bangare a cikin jamiyyar PDP, abin da muke fama da shi, shi ne son  rai. Kuma ko wace jamiyyar na fuskantar irin wannan matsala. Ko daya dai an sami rashin jituwa amma babban abu shi ne ba mu bari rashin jituwar ya haifar da babban rikicin da zai kai ga rarrabuwar kai ba.

“a maimakon hakan, abin da ya faru a Fatakwal a cikin ranakun karshen mako ya tabbatar da cewa PDP zata iya daidaita rikicin dake cikinta. Na yi Imani da cewa wadanda suke ke fatan tabarbarewar al’amuran jam’iyyar PDP ba su ji dadin abin da ya faru a garin Fatakwal ba, saboda mun gudanar da taron da zai kawo sauyi, zai ceci tattalin arzikinmu, da yin garanbawul a harkokin zabe da kuma tausayin al’ummar Najeriya’’ a  cewar Sanata Ekwerenmadu.

 

Abdulkarim Rabiu