An Fara Shirye-shiryen Jana’izar Muhammad Ali

An kai gawar tsohon zakaran damben duniya Muhammad Ali zuwa mahaifarsa domin shirye-shiryen binne shi a wannan Jumma’a da ke tafe.

 

Ana sa ran mashahuran mutane za su hallara a wani gagarimin taro da za a yi domin tuna wa da shahararran tsohon dan damben duniya Muhammad Ali.

 

Daga cikin manyan bakin da za su yi jawabi har da tsohon shugaban Amirka Bill Clinton da kuma dan wasan barkwanci Billy Crystal.

 

Shi dai Muhammad Ali ya bar duniya yana da shekaru 74 da haihuwa, kuma ya kasance cikin shahararrun mutane a karni na 20 da ya gabata.

 

Mutane da dama a duniya dai sun nuna juyayi da alhini da mutuwar ta Muhammad Ali.

 

DW/Abdulkarim Rabiu.