An Hallaka Wata ‘Yar Majalisar Dokokin Birtaniya

An harbe ‘Yar majilisar dokokin kasar Birtaniya mako daya kafin a gudanar da zazzafar muhawarar kuria’ar jin ra’ayin jama,a na ko kasar ta ci gaba da kasancewa cikin kungiyar Tarayyar Turai ko a’a.

 

Wannan lamari ya sa kasar ta yi sanyi a gwiwa, domin ko bata saba ganin harin bindiga ba ko kuma hargitsin siyasa mai muni ba.

 

Wasu wadanda suka ga harbin da a kayi wa wannan ‘Yar majilisar sun ji makashin sai da yayi kuwa ya kira sunan Birtaniya kana ya harbe ta kuma ya kara da daba mata wuka wadda ya harban wato Jo Cox, karamar mamba ce a majilisar dokokin kasar.

 

‘Yar majilisar, yar shekaru 41, mai ‘ya’ya biyu, tsohuwar ma’aikaciyar aikin jin kai ce, kuma sananna ce a fannin yawan magana akan ‘yan gudun hijarar kasar Syria, kana bata boye ra’ayin ta game da ‘yan gudun hijira, kuma tana sahun farko na sukan lamirin cewa Birtaniya ta fice daga kungiyar Tarayyar Turai.

 

Wannan baiwar Allah dai ta mutu duk ko da kokarin da aka yi na ceto ranta , a yankin gundumar ta, a ranar Alhamis.

 

Yanzu haka dai ‘yan sanda na binciken wannan al’amari, sai dai kuma jami’an gwamnati na kafa-kafa da danganta wannan kisa da abinda yake da nasaba da siyasa.

 

‘Yan sandan su kace sun kame wani mutun guda, sai dai basu samu wata kwakkwarar hujjar tuhumar sa ba tukuna, amma kuma suna nan suna neman karin wadanda ake tuhuma.

 

Sakatariyar harkokin cikin gidan Birtaniya ta ce ba zata ce uffan ba game da wannan kisan, har sai an samar da kwakkwaran madogara,

 

Tace kuma akwai bukatar dakatar da wannan muhawara ta ci gaba da kasancewa cikin kungiyar Tarayyar Turai ko kasar ta fice har zuwa wani lokaci.

 

VOA/Abdulkarim Rabiu