An soki yin kurin Toshe kafofin sada zumunta a Ghana

Wakilin sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya, a kasashen Afirka ta Yamma da yankin Sahara, Dokta Muhammed Ibn Chambas ya ce, majalisar ta yi tir da duk wani shiri na toshe kafofin sada zumunta a Ghana.

 

Muhammed Ibn Chambas ya ce, matakin takaita amfani da kafofin sada zumunta zai kawo koma baya ga dimokradiyya a kasar ta Ghana.

 

A watan Mayu ne dai aka ambato supeto janar na ‘yan sandan Ghana yana cewa, suna duba yiwuwar toshe kafofin sada zumunta a duk fadin Ghana, a ranar zaben shugaban kasar, wato 7 ga watan Nuwamba.

 

Wannan batu dai yana ci gaba da janyo kace-nace a Ghana.

 

BBC/Abdulkarim Rabiu