Babu sasanci tsakanin rundunar sojin Najeriya da yan tawayen Naija Delta.

Shugaban rundunar Tsaron Najeriya Janar Olanisakin ya sha alwashin cewa rundunar sojin kasar ba zata sasanta da yan tawayen Naija Delta ba duk kuwa da ci gaba kai hare-haren da suke yi akan bututan mai da na iskar gas.

 

Olanisakin ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a lokacin da yake kaddamar da wasu motocin yaki na zamani guda 10, wadanda za a tura sansanonin soji daban daban dake  fadin  kasar.

 

Har-ila-yau shugaban rundunar tsaron na Najeriya wanda shugaban rundunar sojin sama Air Marshal Sadiq Abubakar ya rufawa baya tare da kwamandan kula da tsare-tsare na sojin sama Air vice Marsharl Sani Ahmed, ya ce babu gudu ba ba jada baya a shirinsu na samar da tsaro a Najeriya.

 

Ya kara da cewa rundunar sojin Najeriya ba za ta nemi sasanci da yan Tawayen Naija Delta ba, kazalika ba zai sassuatawa masu fafutukar neman yancin yankin Biafra ba.

 

’’Akwai hanyoyin da suka fi cancanta su nuna damuwarsu a maimakon daukar wannan mummunan mataki. Hanyar da da fi dacewa ita ce su nemi izinin yin zanga-zangar lumana amma idan suka nuna tashin hankali ba za mu sassauta musu ba” A cewarsa.

 

 

 

Abdulkarim Rabiu.

 

  • ISMAIL AHMAD YALWA NGURU

    wannan mataki da sojon Nigeria suka dauka yayi dai dai