Chadi ta tura sojoji 2,000 zuwa Niger

Kasar Chadi ta tura sojoji 2,000 zuwa Niger domin dakile hare-haren kungiyar Boko Haram a kasar.

 

Wasu majiyoyin soji sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa sojojin sun isa kasar ta Niger ne a ranar Talata.

 

Babu wata majiya daga hukumomin Niger da ta tabbatar da wannan lamari.

 

A karshen makon da ya gabata ne mayakan Boko Haram suka kai hari garin Bosso inda suka kashe sojojin Niger da dama.

 

Akalla mutane 50,000 suka tsere daga yankin, wanda ke da iyaka da Najeriya.

 

Niger da Chadi da Kamaru da kuma Najeriya na aiki tare a yankin Tafkin Chadi domin murkushe ayyukan Boko Haram, wacce ta kulla alaka da kungiyar IS da ke da cibiya a Iraki da Syria.

 

BBC/ Abdulkarim