Dogara ya bukaci Musulmai da su yi amfani da koyarwar watan Ramadan.

Kakakin Majalisar wakilan Najeriya Yakubu Dogara ya bukaci alúmar Musulmin kasar da su yi amfani da watan Ramadan mai tsarki wajen yi wa Najeriya da shugabanni a ko wani matakin gwamnati addu’a ta musamman.

A wata sanar wa da fito daga bakin mai Magana da yawunsa, Turaki Hassan a Abuja babban birnin kasar, kakakin majalisar wakilan yace, ’’ina mutukar bukatar adduói duba da irin halin da tsaro da tattalin arzikin kasar ya shiga.

Mr Dogora ya kuma bukaci  jama’a kada su yi sakaci, kana su jajirce tare da kyakkawan fata na samun sauyi a nan gaba .

“babu wani kalubale da ba za a iya shawo kansa ba ta hanyar addua, da jagorancin Ubangiji. Alúmmomi da kasashe da dama sun fuskanci irin wannan mawuyacin halin fiya da yadda muke fuskanta, amma sun shawo kansu. Don haka namu ma ba a barshi a baya ba, mu ma muna fatan shawo kan namu”. A cewar kakakin majalisar ta wakilan Najeriya.

Ka zalika ya jaddada kudiri da shawarar da majalisar wakilan Najeriyar ta yanke na ako da yaushe zata bayar da fifiko wajen tallafawa mabuka ta da marasa galihu dake cikin alúmma.

 

 

Abdulkarim Rabiu.