Harin Turkiyya ya yi sadiyyar yarukan mutane 36 tare da jikkata 147

Da safiyar Larabar nan ne Fira Ministan kasar Turkiyya Binali Yildirin yayi kira da hada kai, a dai-dai lokacin da mutanen da suka mutu a harin bom da aka kai tashar jirgin saman kasar ke karuwa zuwa 36.

 

Daya daga cikin ‘yan majalisar zartarwan gwamnatin kasar yace cikin adadin da suka mutun harda su ‘yan kunar bakin waken su 3 wadanda suka iso tashar jirgin cikin tasi da yammacin jiya Talata, inda da farko suka shiga budewa mutanen dake zirga-zirga a wannan tashar wuta a harbin mai kan uwa da wabi, kafin daga bisani suka tada bom musammam da suka ga ‘yan sanda sun kusa kai garesu.

 

Babban jami’in yace mutane da yawa sun ji rauni. Da farko mahukunta sunce wadanda suka ji rauni sun kai 60 amma daga bisani adadin ya haura har zuwa 147.

 

Rahotanni sun yi nuni da cewa daya daga cikin ‘yan kunar bakin waken ya tada nasa bom din ne a wajen tashar jirgin inda mutane ke sauka daga jirgi.

 

Kuma wannan wurin sau tari zaka taras da shi cike da jamaá suna jiran abin hawa, kana sauran biyun kuwa an yi imanin cewa sun yi kokarin shiga cikin tashar wanda take cike da ‘yan sanda amma basu samu nasarar hakan ba.

 

Sai dai kawo yanzu ba wanda ya dauki alhakin aikata wannan danyen aikin, wanda yazo dai-dai da lokacin da gwamnatin kasar take fama da tagwayen barazanar masu tsananin kishin addini dake kudu maso gabashin kasar.

 

VOA/ Abdulkarim Rabiu