INEC zata kammala zabubbukan da a aka dakatar kafin 21 ga watan Yuli

Hukumar zabe mai zaman Kanta ta kasa a Najeriya (INEC) ta bayyana cewa zata kammala zabubbukan da aka dakatar a jihohin Rivers, Imo, Kogi da Kano nan da zuwa 31, ga watan yulin 2016.

Bayanin  hakan na kunshe a cikin wata sanarwa da babban daraktan sahen wayar da kai da ilimantar da masu kada kuria na hukumar zaben ta INEC, Mr Oluwole Osaze-Uzzi.

Hukumar zabe ta na gabatar muku da wannan sanarwa da ta kunshi tsarin yadda za a daidaita rikicin da ya yi sanadiyyar dage zabubbuka a yankunan da abin ya shafa.

’’ hukumar ta karbi korafe-korafe daga jam’iyyun siyasa daban-daban, da ‘yan takara da kuma masu ruwa da tsaki, kuma ta tuntubi hukumomin tsaro agame da hanyoyin samun masalaha.

‘’ bayan yin nazari akan binciken da aka gudanar, hukumar ta bayyana bukatar da ke akwai ta neman shawarar masu ruwa da tsaki da hukumomin tsaro musaman daga jihohin da al’amarin ya shafa.

’’ har-ila-yau hukumar ta bayyana bukatar dake akwai ta neman goyan bayan kungoyin kwararru a fannin samar da zaman lafiya da kuma sulhunta rikici.

’’Kazalika hukumar zaben ta bayyana fatan samun kyakyawan yanayi na gudanar da zaben kafin nan da karshen  watan Yulin 2016.’’

Kwamishinan zaben ya kuma gabatar da jadawalin da kuma tsarin yadda zaben zai wakana kuma ya bukaci goyan bayan dukkannin masu ruwa da tsaki.

 

 

Abdulkarim Rabiu