Kungiyar Mi yetti Allah ta nisanta kanta da harin jihar Enugu.

Shugaban kungiyar Mi yetti Allah kautal hore a tarayyar Najeriya, Alhaji Bello Bodejo, ya ce kisan samamen da ya faru a jihar Enugu dake kudancin Kasar abun takaici ne kwarai matuka.

Ya ce wani abu da ya fi shi muni shi ne kokarin da a ke yi kota halin kaka a alakanta Fulani makiyaya da wannan mummunan aiki, duk kuwa da masu ruwa da tsaki a fannin tsaron jihar sun gudanar da bincike.

Shugaban ‘yan sandan jihar ya fito karara ya nisanta Fulani makiyaya da wannan ta’asa amma har yanzu wasu ‘yan kasar na ci gaba da yunkurin gogawa Fulanin kashin kaji dangane da mummunan al’amarin.

“tsakanin fulani makiyaya da manoma tamkar Danjuma ne da Danjummai a don haka ya zama tilas a rinka hakuri da juna, duk kuwa da cewar tsakanin harshe da hakori ma akan sami sabani, amma a duk lokacin da irin wannan al’amari ya faru a guji daukar doka a hannu domin yin hakan shi ke haifar da da na sani a tsakanin al’umma”. In ji Alhaji Bello Bodejo

Shugaban Kungiyar ya shawarci Fulani makiyaya da su kara azama wajen kafa kungiyoyin sa kai domin taimakon kai da kai a tsakanin su.

Kazalika ya hori takwarorinsa jagororin kungiyar da su guji hassada a tsakaninsu domin kuwa hannu daya baya daukan jinka.

Da ya juya batun yankin Arewa maso gabashin Najeriya kuwa, ya yabawa dakarun sojin Najeriya a kokarinsu na maido da zaman lafiya a yankin.

Har-wa-yau ya shawarci ‘yan Najeriya da su ci gaba da yin addu’a ga gwamnatin Najeriya, domin a cewarsa tana da kyawawan manufofi.

Abdulkarim Rabiu/Musa Aminu