Majalisar dattawan Najeriya ta nemi a kawo karshen hare-haren Fulani makiyaya.

Shugaban masu rinjaye a majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ali Nndume ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba majalisar za ta yi mahawara a kan yanda za a kawo karshen hare-haren da ake zargin makiyaya na kai wa a wasu kauyuka.

yayin da yake zantawa da manema labarai a  Fadar shugaban kasa dake Abuja babban birnin kasar, ya bukaci alúmmomin kasar da su bayar da bayanai masu amfani agame da batun.

“makon da ya wuce majalisar ta gabatar wani kudirin doka agame da wannan batu a matsayin abin da ke bukatar daukar matakin gaggawa, kuma ta kafa kwamiti na musanman karkashin jagorancin Sanata Ndume domin yin nazari da kuma gaggauta kawo karshen wannan alámari da yaki ci ya ki cinye wa. Muna rokon jamaá su fito fili karara su bamu bayani da kuma shawarwari akan yadda za a shawo kan wannan alámari kafin ya tabarbare” in ji Sanata.

Ya ce ya kamata a gurfanar da wadanda aka kama da laifi yayin da kuma ya bukaci Karin goyan baya daga alúmmomin yankin arewa maso gabas.

“” ba ma so mu kawo batun addini ko kabilanci akan wannan batu, domin ta haka ne ya sa aka kasa kawo karshen rikicin Boko Haram. Ba ma so mu kara yin irin wannan kuskure. Wajibi ne a hukunta duk wadanda su ka aikata irin wadannan laifuka. Mutanen nan masu laifi ne, bai kamata a fara cewa Fulani ne ba saboda a ko da yaushe Fulani su na dauke da sanda ko adda da suke sare ganyayyaki domin anfanin dabbobinsu, amma wadannan mutane da suke kai hari suna dauke da bindigogi samfurin AK 47.” In ji Sanata Ndume.

 

Sanata Ndume yace ya yi daidai da aka kama  wasu daga cikin wadanda ake zargin sannan idan an gudanar da cikakken bincike gaskiya za ta bayyana.

 

Kazalika, ya yi amfani da wannan damar ya mika godiyarsa ga  gwamnatin Najeriya da hukumomin bayar da agaji dangane da taimakon da suka bai wa alummomin yankin arewa maso gabas. Bugu da kari ya nemi Karin tallafi musam ma na  kayayyakin abinci domin amfanin wadanda rikicin Boko Haram ya daidaita.

 

Abdulkarim Rabiu.