Majalisar wakilai ta bukaci ministan ayyukan gona ya bayyana a gabanta.

Majalisar wakilan Najeriya ta bukaci ministan ayyukan Gona, Audu Ogbeh da ya bayyana agabanta don yin bayani akan dalilin da ya sa ake sayar da kayan amfanin gona da ake sanya musu maguguna domin su yi saurin girma a kasuwannan Najeriya wadanda kuma ake zargin suna harfar da ciwon sankara wato Cancer a turance.

Har-wa-yau majalisar ta bukaci babban darantan hukumar kula da ingancin abinci da magunguna wato NAFDAC da ya gabatar mata da jerin sunayen magunguna da kuma kayan amfanin gonar da ake sanya wa irin wadannan magunguna wadanda hukumar ta yi wa rijista.

Bukatar hakan ta biyo bayan wani kudirin doka da aka gabatar da ya nuna cewar wadannan sinadarai na da illa mutuka ga rayuwar biládama.

Da yake gabatar da kudirin dokar wanda kuma ya sami goyan baya, Mr Austin Chukwukere ya bayyana damuwarsa dangane da yadda Hukumar kula da sahihanci kayyakin amfani gona ta bai wa kamfanin samar da magugunan amfani gona na Monsanto Agriculture Nigeria Limited lasisin sayar da auduga wadda aka noma da irin wadannan sinadarai a kasuwannin Najeriya.

 

 

Abdulkarim Rabiu